96.The Clot

  1. Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta
  2. Ya hahitta mutum daga gudan jini
  3. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci
  4. Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami
  5. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba
  6. A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu)
  7. Dõmin yã ga kansa, yã wadãta
  8. Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take
  9. Shin, kã ga wanda ke hana
  10. Bãwã idan yã yi salla
  11. Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya
  12. Ko ya yi umurni da taƙawa
  13. Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya
  14. Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani
  15. A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa
  16. Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi
  17. Sai ya kirayi ƙungiyarsa
  18. Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma)
  19. A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka)