37.Those drawn up in Ranks
- Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi)
- Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi
- Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa
- Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne
- Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã
- Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri
- Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai
- Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe
- Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya
- Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi
- Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri
- Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili
- Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa
- Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili
- Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne
- Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne
- Ashe kõ da ubanninmu na farko
- Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu
- Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi
- Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako
- Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa
- Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa
- Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm
- Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne
- Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna
- Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne
- Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna
- Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)
- Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba
- Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka
- Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne
- Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu
- To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar
- Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi
- Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai
- Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci
- Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni
- Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne
- Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa
- Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake
- Waɗannan sunã da abinci sananne
- Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa
- A cikin gidãjen Aljannar ni'ima
- A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna
- Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari
- Farã mai dãɗi ga mashãyan
- A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba
- Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu
- Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye
- Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna
- Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)
- Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne
- Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne
- (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)
- Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim
- Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni
- Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)
- Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba
- Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba
- Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma
- Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa
- Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm
- Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai
- Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm
- Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne
- To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta
- Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi
- Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take
- Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu
- Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa
- Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu
- Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu
- Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance
- Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake
- Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu
- Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba
- Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa
- Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe
- Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu
- Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa
- Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai
- Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu
- Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake
- A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya
- A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa
- Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa
- To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu
- Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri
- Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne
- Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya
- Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba
- Me ya sãme ku, bã ku magana
- Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma
- Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa
- Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa
- Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa
- Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm
- Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci
- Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni
- Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne
- Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri
- To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri
- Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago
- Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm
- Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa
- Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna
- Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma
- Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe
- Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm
- Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa
- Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai
- Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne
- Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin)
- Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna
- Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma
- Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya
- Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni
- Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya
- Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe
- Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna
- Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa
- Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai
- Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni
- A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba
- Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta
- Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko
- Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã)
- Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake
- Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe
- Aminci ya tabbata ga Ilyãs
- Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa
- Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai
- Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni
- A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya
- Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba)
- Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen
- Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci
- Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba
- Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni
- A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi
- Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya
- Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi
- To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba
- Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su
- Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya
- Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi
- Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka)
- Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci
- Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza
- Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce
- To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa
- Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne
- Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza
- Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)
- Shin, bã ku tunãni
- Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne
- To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya
- Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã)
- Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa
- Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake
- To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa
- Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi
- Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm
- Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne
- Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)
- Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi
- Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa
- Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko
- Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake
- Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani
- Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni
- Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako
- Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya
- Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci
- Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani
- Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa
- To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana
- Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci
- Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa
- Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa
- Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni
- Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu