36.Yaseen

  1. Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni* Mai hikima
  2. Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikin Manzanni
  3. A kan hanya madaidaiciya
  4. (Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai
  5. Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne
  6. Lalle, haƙĩƙa, kalma* tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba
  7. Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne
  8. Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani
  9. Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba
  10. Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci
  11. Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani
  12. Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni* suka jẽ mata
  13. A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku
  14. Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi
  15. Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku
  16. Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne
  17. Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku
  18. Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi
  19. Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan
  20. Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne
  21. Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku
  22. Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã
  23. Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna
  24. Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni
  25. Aka ce *(masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani
  26. Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama
  27. Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama* a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba
  28. Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu
  29. Yã nadãma a kan bãyĩ Na! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili
  30. Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba
  31. Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurin Mu
  32. Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci
  33. Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta
  34. Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba
  35. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba
  36. Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu
  37. Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani
  38. Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa
  39. Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo
  40. Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi
  41. Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa
  42. Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba
  43. Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci
  44. Kuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku
  45. Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta
  46. Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya
  47. Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya
  48. Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma
  49. Bã zã su iya yin wasiyya* ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba
  50. Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu
  51. Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya
  52. Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu
  53. To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa
  54. Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi
  55. Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira
  56. Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo
  57. Aminci," da magana,* daga Ubangiji Mai jin ƙai
  58. Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi
  59. Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne
  60. Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya
  61. Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba
  62. Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita
  63. Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci
  64. A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa
  65. Dã Mun so, dã Mun shãfe gani *daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani
  66. Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba
  67. Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta
  68. Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne
  69. Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai
  70. Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su
  71. Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci
  72. Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba
  73. Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su
  74. Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã)
  75. Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa
  76. Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar
  77. Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu
  78. Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne
  79. Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi
  80. Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi
  81. UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi)
  82. Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku