26.The Poets

  1. S̃. M̃
  2. Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne
  3. Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba
  4. Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai
  5. Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa
  6. To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu
  7. Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau
  8. Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba
  9. Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama
  10. Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai
  11. Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba
  12. Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni
  13. Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci* kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna
  14. Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni
  15. Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre
  16. Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne
  17. Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu
  18. Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka
  19. Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai
  20. Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi
  21. Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni
  22. Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla
  23. Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu
  24. Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni
  25. Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba
  26. Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko
  27. Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne
  28. Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta
  29. Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru
  30. Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa
  31. Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya
  32. Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne
  33. Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo
  34. (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi
  35. Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa
  36. Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne
  37. Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani
  38. Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne
  39. Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne
  40. Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya
  41. To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya
  42. Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai
  43. Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa
  44. Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya
  45. Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya
  46. Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada
  47. Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta
  48. Ubangijin Mũsa da Hãrũna
  49. Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya
  50. Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu
  51. Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni
  52. Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã* ne
  53. Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne
  54. Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan
  55. Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne
  56. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne
  57. Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari
  58. Da taskõki da mazauni mai kyau
  59. Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla
  60. Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã
  61. Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne
  62. Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni
  63. Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,* kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma
  64. Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can
  65. Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya
  66. Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen
  67. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
  68. Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai
  69. Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm
  70. A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa
  71. Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su
  72. Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira
  73. Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku
  74. Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa
  75. Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa
  76. Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa
  77. To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu
  78. Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni
  79. Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni
  80. Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni
  81. Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni
  82. Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako
  83. Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai
  84. Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutãnen ƙarshe
  85. Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima
  86. Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu
  87. Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su
  88. A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi
  89. Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki
  90. Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa
  91. Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku
  92. Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa
  93. Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu
  94. Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun
  95. Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya
  96. Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma
  97. Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna
  98. A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu
  99. Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi
  100. Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta
  101. Kuma bã mu da abõki, masõyi
  102. Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai
  103. Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba
  104. Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
  105. Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni
  106. A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba
  107. Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce
  108. To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  109. Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu
  110. Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  111. Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka
  112. Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa
  113. Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa
  114. Ban zama mai kõre mũminai ba
  115. Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa
  116. Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa
  117. Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni
  118. Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai
  119. Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi
  120. Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran
  121. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba
  122. Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama
  123. Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni
  124. A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba
  125. Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce
  126. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  127. Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu
  128. Shin, kunã yin ginin sitadiyo* a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa
  129. Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama
  130. Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa
  131. To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  132. Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani
  133. Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya
  134. Da gõnaki da marẽmari
  135. Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma
  136. Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba
  137. Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen* mutãnen farko
  138. Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba
  139. Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
  140. Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
  141. Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni
  142. A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba
  143. Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce
  144. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  145. Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu
  146. Shin, anã barin ku* a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu
  147. A cikin gõnaki da marẽmari
  148. Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi* mãsu narkẽwa a ciki
  149. Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari
  150. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  151. Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata
  152. Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa
  153. Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake
  154. Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya
  155. Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan* yini, kuma kunã da shan yini sasanne
  156. Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku
  157. Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma
  158. Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba
  159. Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
  160. Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni
  161. A lõkacin da ɗan'uwansu,* Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba
  162. Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce
  163. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã
  164. Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu
  165. Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai
  166. Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa
  167. Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)
  168. Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa
  169. Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa
  170. Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya
  171. Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa
  172. Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu
  173. Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana
  174. Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba
  175. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
  176. Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni
  177. A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba
  178. Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce
  179. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã
  180. Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu
  181. Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)
  182. Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce
  183. Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna
  184. Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko
  185. Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne
  186. Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata
  187. To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya
  188. Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa
  189. Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije* ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma
  190. Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba
  191. Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
  192. Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne
  193. Rũhi* amintacce ne ya sauka da shi
  194. A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi
  195. Da harshe na Larabci mai bayãni
  196. Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko
  197. Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi
  198. Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa
  199. Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba
  200. Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi
  201. Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi
  202. Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba
  203. Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne
  204. Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa
  205. Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru
  206. Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu
  207. Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare* su
  208. Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi
  209. Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba
  210. Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba
  211. Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa
  212. Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne
  213. Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba
  214. Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci
  215. Kuma ka sassauta fikãfikanka* ga wanda ya bĩ ka daga mũminai
  216. Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa
  217. Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai
  218. Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye
  219. Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada
  220. Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani
  221. Shin, (kunã so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka
  222. Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi
  223. Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne
  224. Kuma mawãƙa* halakakku ne ke bin su
  225. Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba
  226. Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa
  227. Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa