25.The Criterion

  1. Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta
  2. wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkin Sa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa
  3. Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa
  4. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana
  5. Kuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma
  6. Ka ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai
  7. Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi
  8. Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce
  9. Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki
  10. Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje
  11. Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a
  12. Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta
  13. Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can
  14. Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa
  15. Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma
  16. Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka
  17. Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya
  18. suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku
  19. To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma
  20. Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani
  21. Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma
  22. A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe* mu
  23. Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya
  24. Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla
  25. Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa
  26. Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani
  27. Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo
  28. Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba
  29. Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum
  30. Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa
  31. Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako
  32. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa
  33. Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara
  34. Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya
  35. Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi
  36. Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yin Mu." sai Muka darkãke su, darkãkewa
  37. Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai
  38. Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa
  39. Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa
  40. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma)
  41. Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo
  42. Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya
  43. Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa
  44. Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida* suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya
  45. Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta
  46. Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi
  47. Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma)
  48. Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamar Sa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama
  49. Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta
  50. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa* shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci
  51. Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kõwace alƙarya
  52. Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma
  53. Kuma shĩ ne Ya gauwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa
  54. Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi
  55. Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa
  56. Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi
  57. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa
  58. kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa
  59. Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi
  60. Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana* ta ƙãra musu gudu)
  61. Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta
  62. Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde
  63. Kuma bãyin Mai rahama* su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya)
  64. Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu
  65. Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra
  66. Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni
  67. Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa
  68. Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka
  69. A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce
  70. Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai
  71. Kuma wanda ya tũba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah
  72. Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci
  73. Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame* da makãfi
  74. Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya* mu shũgabanni ga mãsu taƙawa
  75. Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci
  76. Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni
  77. Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku* ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci